Page 11
"Ban taba jin ciwon ba ni da ya mace ba irin yau, amma ko'ina da 'ya macen ma, yaya ka san, babu aure tsakaninta da Musaddik tunda Musaddik ya riga ya sha nono na, amma yaya me ka gani akan shawarata?" Mallam Mahmud ya dubeta ya ce "Shawararki ta yi, abar kuma dubawa ce, kuma kada ki kara tunanin ba ki da 'ya mace, domin 'yayana naki ne haka zalika hada Musaddik aure da yar’uwar shi kadai ya kamata, domin 'yar-uwarsa ita kadai ce zata rufa masa asiri, za kuma ta yi hakurin zama da shi”. Inna Halima Ta ce "'Haka ne". Ya ce "Saboda haka, zan hada shi da Na'ima, tunda ita ce gaba da Afrah, Inna Halima ta yi murmushi sosai. tace “Allah ya saka da alheri ya kara dankon zumunci, yasa sanadiyyar shiryuwarsa ce” Yace "Haba Halima wannan duk yi ma kai ne, na kuma gode da wannan tunanin naki, wanda ni ban yi irinsa ba, na kuma ba ki damar ki yi magana da Musaddik ki gaya masa hukuncin da muka yanke" Ta ce “In sha Allahu zan yi magana da shi." Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa na dan wani lokaci kafin su yi sallama ta tafi, ba tare da sun gaisa da Mama Hauwa ba, yadda ba ta fito sun gaisa ba, haka nan ita ma ba ta bita daki sun gaisa ba, dama sun saba yin hakan.