Page 12
Washegari bayan sallar azahar, Afrah na zaune tana wanke-wanke. Na'ima kuwa dawowarta kenan daga gidan kitso, tann zaune akan kujera Yar tsuguno tana latse-latsen waya. Mallam Mahmud ya yi sallama ya shigo. ya dawo daga masallaci, cike da tausayawa ya dubi A frah ya ce. "Sannu da kokari, har yanzu ba ki samu hutawa ba, kin yi sallah dai ko?" Ta amsa “Na yi sallah Baba” ya jinjina kai zai wuce “Sannu da zuwa” Cewar Ni'ima, ya dubeta fuska tamke ya ce. "Yauwa, ke ba kya aikin komai ne?" Kafin ta yi magana Mama Hauwa ta cafke a lokacin da ta Ke fitowa daga daki "Ta gama nata, ko shi ma aikin sai ansa ido a kansa?” Bai Kara magana ba har ya isa kofar dakinsa, sannan ya Kwala ma Mama Hauwa kira, kai tsaye ta nufo inda yake ba tare da ta amsa ba. "Ga-ni” ya dubeta gami da girgiza kai sannan ya ce. "Ba ni abin zama, magana za muyi me muhimmanci” Nan ma ba ta amsa ba, ta shige ta dauko. tabarma ta shimfida masa ya zauna, ita kuma ta jingine jikin katanga tana kallonsa. "Wace magana za mu yi?" Ya ce a yayin da yake kallonta "Ina bukatar natsuwarki, domin magana za mu yi kamar yadda na gaya miki kuma me muhimmanci ce maganar” tace "To ai ina jinka." Yace “Dama maganar Na'ima ne, ina ganin lokaci ya yi daya kamata