Musabbabi Book 1

Page 13

by @yargidanimam

ace ta yi aure, don haka na yanke shawarar ni da Halima akan zan hada ta aure da Musaddik”, Haka nan Afrah ta ji gabanta ya fadì, wanda ta rasa dalilin hakan, sai dai ta ji ta sami kanta da matukar tausayin "yar-uwarta, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma ya zama dole ta tausaya mata, domin ta san auren miji irin Musaddik hakika rashin dace ne ga ko wace ya mace. Mama Hauwa ta zaro idanu waje, tamkar za su fado kasa, bakinta na tsuma ta ce "Wane Musaddik din?” Yana kallonta yace "Musaddik din har nawa garemu? Musaddik dai nawa mana” Mama Hauwa ta saki salati tana tafa hannu, Tace “Eh, sai yau na kara tabbatar da cewa Malam baka son yayana,sannan Halima ba zata taba barina na zauna lafiya ba, yau ko maza sun kare kaf a duniya. Me Na'ima za ta yi da Musaddik? Sakaran yaro mara natsuwa, babu wanda bai san halin da yake ciki ba na barbada, da can sanda yake na kwarai me ya, sa ba ka yi tunanin hada shi auran da "yarka ba, sai yanzu daya zama lalatacce. Sanda yake da kumbar susa yake shiga mota yana fita, ai ba ka ce za ka ba shi 'yarka ba, duk da a lokacin har tayin Sakina na yi maka, akan ya aureta Ka ce ya riga ya sami mata, ba kuma zaka tursasa masa ba, yanzu ina matar, halinsa ya koreta, ya zama shakulatin bangaro,