Page 14
sai da ya zama mara amfani shine za ka ce Na'ima ta aure shi, to ba ka isa ba." Malam Mahmud ya nuna kansa ya ce "Ban isa ba a matsayina na ubanta?" Ta turo baki. "Eh, in dai akan wannan maganar ne ba ka isa ba, kada ma ka kara furtawa. Na'ima ta fi karfin Musaddik, ko shi ne autan maza ba za ta aure shi ba." Mallam Mahmud ya fusata ya ce. "To zan ga wanda ke da iko da ita tsakanin ni da ke, domin na riga na gama magana, na ba Musaddik Na'ima.” Mama Hauwa ita ma ta fusata, bakinta na kumfar masifa tace "To za mu ji, za mu gani, wai an binne tsohuwa da rai, domin in dai ina raye Na'ima ba zata auri wannan tambadaddan yaron ba, aniyarku duk zata bi ku kai da Haliman” Ta juya fuuu! Ta tafi. Malam Mahmud ya tashi ya bude dakinsa ya shiga cike da matukar bacin rai. A yayin da Na'ima ta saki tsaki ta mike tana turo baki, tana kallon Mama Hauwa "Allah Ya yi min tsari da wannan mutumin, lallai babu kauna tsakanina da Baba”, Mama Hauwa ta yi tsaki ita ma ta ce "In dai kauna ce, ai baya kaunarmu gaba daya. Musaddik din me. Allah ya tsari gatari da saran Shuka, wuce ki shiga daki” Na"ima ta shige daki tana surutai na rashin tarbiyya da ilimi. Haka Mama Hauwa ta wuni a cikin gidan tana sababi, wanda duk akan Afrah ya kare.
Ku dakace ni
YAR GIDAN IMAM
Bayan yarda da rashin comments ba, wallahi ina iya daina posting din idan ba zaku dinga yin comments ba. MUSABBABI
NA
HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM
***