Page 15
harara da hantara da sa aiki duk Afrah ta sha su a ranar, don dai Mallam Mahmud ya tanka, ta kara juye kwandon masifarta a kansa, duk dalilin haushin hukuncin daya yanke akan Na'ima,
A yayin da Inna Halima a ranar dai ta nemo Musaddik ta zauna da shi, ta yi masa bayanin duk hukuncin da suka yanke a kansa. Musaddik ya mumfasa gami da kallon Inna Halima. Sannan ya ce "Anya Inna ki na ganin Mama Hauwa za ta amince da wannan maganar, idan
akayi la'akari da abinda ya faru a baya a game da sakina kuma ki na ganin ita kanta Na'ima za ta yarda ta aureni, a halin da na ke ciki a yanzu?" Inna Halima ta gyara zama cike da damuwa tace "Wannan duk ba damuwarka bace, kawai kai ma na gaya maka ne saboda ka sani, ba don mu zauna muna tattaunawa ba, abinda muka yanke kenan saboda wannan halin da kake yi ya na neman ya tagayyara duk kan tunanin mu, muna tunanin kuma wannan hanyar itace kadai zata iya taimakon mu dawo da kai hanya madaidaiciya, don haka babu ruwanka da abinda Hauwa zata yi, tunda Na’ima ba yarta bace ita kadai ba”. Ya gyada kai fuska cike da jimamin wai yau shine ake nema masa matar aure sabida babu wacce zata iya da shi, idan ya tuna yadda mata ke turo kansu a da wajensa, yakan ji komai ya tsaya masa a rai. A hankali Yace “Shi kenan Inna. Allah ya yi mana zabin abinda ya fi zama alheri, nagode da kokarinku a gare ni”
Ta jinjina kai, cike da karin tausayinsa ta ce “Amin Allah kuma ya sa sanadiyya ce ta shiryuwarka, Allah ya rabaka da wannan 'mummunan halin, ya dawo maka da matsayinka na da “ Ya amsa a sanyaye, “Amin” sannan ta kara dubansa tace, "Zuwa yau da daddare ko gobe ina son ka bulla gidan Kawun naka, domin ka yi magana da Na'ima ka kuma samu Kawun naka, ka yi masa godiya tare da nuna masa amincewarka akan hukuncin mu” Yace “To zan yi kokarin yin hakan."ta zuba masa ido sosai tace “Musaddik yaushe rabonka da wanka? Ka ga kayan jikinka , me yasa kake kokarin maida kanka mahaukaci ne” shuru ya yi ya maida kansa kasa , ta aje numfashi tace “Baka da sabulun wanka da wankin ne”, ya gyada kai alamar eh ba tare da ya yi magana ba tace “Amma ba ni nace ka dinga zuwa kana yin wanki ba,har cewa nayi ka dinga dakko wankin kana kawowa gidana ni zan dinga yi maka, irinku ba a wofintar da ku ajiiki ya kamata a dinga janku , na gaya maka duk damuwarka ka dinga zuwa kana gaya min” idanunsa cike da hawaye ya mike tsaye ya juya baya saboda baya son ta ga hawayensa , Yace cikin muryar kuka yana magana yana tafiya, “zan zo nayi wankin gobe inna”daga nan ya yi sallama da ita ya fice daga gidan.