Page 17
Domin duk wanda Allah ya Batar, babu wanda ya isa ya shiryar da shi, haka zalika duk wanda ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi. Idan ki na tuna haka, ba za ki taba samun damuwa ba. Da ai ba haka yake ba, don haka a yanzu ma wata kaddarar ce ta hau kansa, wacce sai an dage kwarai da addu’a”. Afrah ta gyada kai cike da jindadin nasihar malaminta, wanda hakan yana daya daga cikin dalilan da ya sa take matukar sonsa, ta ce, “Naji ya Sayyadi, nagode kwarai da nasiharka, na kuma yarda da duk abinda ka fada, sai dai ina rokon kai ma ka dinga sa Dan-uwana cikin addu"arka da bakinka me cike da ambaton Allah” Ya yi murmushi ya ce "Zan sa shi a cikin dukkan addu'oi ta Afrah. Allah ya shiryemu gaba daya." Ta amsa "Amin, nagode",
Hayaniyar da Afrah ta jiyo tana tashi daga cikin gidan, ya tilasta mata yin sallama da Mallam Habib, domin ba ta son ya fahimci akwai matsala a cikin gidan, bayan sun yi sallama. Da sauri Afrah ta shige cikin gidan hankalinta a tashe , muryar Mallam Mahmud cike da fusata yake cewa, “Na gaya miki ki yi shiru ko, Na’ima dai ya ta ce, ina da damar da zan aura mata duk wanda na ga dama ko da dan kashin kasuwa ne, karewar lalacewa, ke wace ce da za ki dakatar da ni?" Cewar Malam Mahmud da yake tsaye ransa a matukar bace. Musaddik na tsugunne a gabansa.