Musabbabi Book 1

Page 18

by @yargidanimam

Mama Hauwa na dogare a jikin katanga, ta yi zufa ta yi kasharban saboda tsabar masifa. Afrah na shigowa ta jingina da jikin kofar dakinta, idanunta sun cika da hawaye. Don ta tsani damuwar da take gani a idanun mahaifinta, kamar yadda ta tsani muzantar da ta ga Musaddik ya yi a tsugunne. Mama Hauwa ta ta ja tsaki tace “Duk abinda za ka fada, sai dai Ka fada amma ba zan taba nade hannu na zauna nasa maku ido kuna kokarin nakasa rayuwar 'yata ba, don haka Musaddik ka tattara ka tafi. Duk abinda Kawunka ya fada, ka watsar da shi, don ba mai yiwuwa bane, zan kuma yi mummunan saba maka matukar ka matsa sai ka auri "yata, babu ruwan biri da gada, don haka ina mai gargadin ka da ka dauki maganar da na ke gaya maka, don ita ce hanya me bullewa a gareka. Ka koma can gun tsohuwar matarka da ta talautaka ta kuma gudu ta bar ka, bayan ka zama abinda ka zama. Wacce ta sa ka zabeta, ka bar Sakina, iya rashin kunya yau ina ganinta, to ba dai Na'ima ba, ka kara gaba”. Idanun Musaddik jawur! Ya dago ya dubi Malam Mahmud ya ce "Kawu na gode kwarai da niyyar da kayi na kuma kara tabbatar da cewa ba ni da wanda ya fi ku kai da Inna Halima, domin wannan abinda kake son yi babu me yi min shi sai wanda ya ke matukar kaunata, don duk macen da zata iya aurena yanzu da kuma mahaifin da zai iya ba ni yarsa na aura to sai nasu karfin imani”

Ya maida bakincikin da yake yunkuro masa ya cigaba da cewa “ Duk abinda mama Hauwa ta fada gaskiya ne ban cancanci Na’ma ta aure ni ba , haka kuma ba ni da wata cancantar daya kamata ace na sami mata me cikar kamala,