Page 19
bayan ni ba ni da wannan cikar kamalar, gaskiya ne ko wace uwa tana bufatar farin-cikin 'yarta, don haka Mama Hauwa ba ta da laifi don ta hangi rashin farin-ciki ga "yarta bayan ta aureni". Ya Kara kallonsa, bayan ya ajiye numfashi. sannan ya ci-gaba da cewa, "Saboda haka abar wannan maganar, ni aure ma baya gaba na, kuma bazan boye maka ba bani da wani sha'awar yin aure a yanzu, domin babu yarinyar da na ke bukatar na cutar da rayuwarta Zamana ba wani a karkashina ya fi min kwanciyar hankali, don haka Kawu abar maganar nan kawai don Allah “ Kalamansa sun yi matukar ba Afrah tausayi, nan da na hawayen da take kokarin mayarwa suka suka balle a kumatun ta. Mama Hauwa ta dubi Mallam Mahmud daya sandare a tsaye, komai ya tsaya masa cak! Don bakin-ciki da damuwa. Mama Hauwa Ta watso ma musaddik harara sannan ta dawo da kallonta ga Mallam Mahmud tace “To ka ji yaro, ashe akwai sauran tunani a kansa, abin mamaki ma sai na ga yana neman Yafi Kawun nasa zurfin tunani, domin duk abinda ya fada gaskiya ne. Don haka ya rage naka, kai ma ka'aje makaman yakin naka, kai da kanwar taka da take zuga ka”. Tana gama fadan hakan, daga nan ta juya a fusace ta shige dakinta dai- dai an fara kiran sallar magariba.