Page 20
Mallam Mahmud ya a saki ajiyar zuciya sannan shi ma ya durkusa a gaban Musaddik yana kallonsa, ya dagoshi gaba daya suka tashi tsaye, yana kallonsa ido cikin ido. Musaddik ya ce "Kada ka sa ma kanka damuwa Kawu, ka bar maganan nan, komai lalacewata, ina da tabbacin ba zan rasa wacce za ta iya sona domin Allah ba” Malam Mahmud ya girgiza kai ya ce. Cikin matukar fusata, “Ina nan fa akan bakata, na riga na yi alkawarin sai na aura maka ya ta ,a cikin wannan halin da ka ke ciki kana bukatar kulawa ba daga bare ba, daga Yar’uwa, don haka kada ka yi tunanin zan tashi akan maganata, yanzu ka wuce ka yi alwala, mu tafi masallaci mu yi sallar magariba, sannan ka tafi gida, zan nemeka da kaina idan na gama daidaita komai” Da sauri Afrah ta goge hawayenta ta wuce da sauri ta dauko buta guda biyu ta cikosu da ruwa tazo ta aje, daya a gaban mahaifinta, daya a gaban yayanta. Malam Mahmud ya dago ya zuba mata ido a hankali ya ce "Sannu Afrah. Shi ma Musaddik din kallonta kawai yake ba tare da ya ce mata komai ba, ya ja butar ya fara alawala.duk da yasan akwai bashin salloli a kansa ba, amma baya son kawunsa ya fahimci hakan.’
Ita ma Afrah ta wuce a hankali zuwa dakinta, kasancewar tana fashin sallah, hankalinta a tashe yake tana matukar jin tsoron rayuwar, duniya musamman idan ta tuna yadda Musaddik yake ada da yadda ya koma a yanzu.
Ku dakace ni
Yar gidan imam Rashin yin comments tabbas zai iya sawa na bar yin wannan posting din. MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️
***