Page 21
da yadda kuma mata ke kokuwar kawo kansu gare shi, amma yau saboda canjin yanayi , mace daya da za ta so shi ta zauna da shi, ya rasa. Shi kansa Musaddik bai taba Bata lokaci ya tsaya ya yi tunanin rayuwarsa da makomarta ba. irin daran wannan rana, ya dade yana nemar ma kansa amsar dalilin canjawar rayuwarsa, amma har yanzu ya rasa amsa, da ba haka yake ba. Babu kuma dalilin da zai sa ya koma haka a yanzu, shin wace irin rubutacciyar kaddara ce Allah ya rubuta masa? Sai dai duk da haka yana addu’ar Allah ya ba shi ikon cinye wannan jarabawa.
Washegari tun hantsi Mama Hauwa ta kwashi jiki zuwa gidan Inna Halima da kashedin ta fita harkar ta da ita da 'yarta, anan ma Inna Halima da Mama Hauwa sun kwashi 'yan kallo, don babu wanda ya raga ma wani a tsakaninsu, kaca-kaca su ka yi cikin diban albarka. Mama Hauwa ta bar gidan Inna Halima, tana komawa gida ta shirya Na'ima ta ba ta kudin mota ta ce ta tafi can garinsu, wato Suleja, gidan kakanninta ta zauna can, sai ta gama da lamarin Malam Mahmud. Sai ta tabbatar ya sauko daga maganganunsa, sannan ta dawo, ai ko nan da nan Na'ima ta shirya ta tafi abin ta, ba tare da Malam Mahmu* ya sani ba.