Musabbabi Book 1

Page 22

by @yargidanimam

Har sai bayan ya dawo daga sallar Issha'i Inna Halima ta zo ta gaya masa duk wulakanci da diban albarkar da Mama Hauwa ta je ta yi mata har gida. Kwarai da gaske ran Malam Mahmud idan ya yi dubu ya baci, a fusace ya kira Mama Hauwa ta fito, tana yamutse-yamutse ta dogare a tsaye ta ce "Ga-ni menene?" Malam Mahmud ya dubeta rai bace ya ce "Wai ke Hauwa me ki ke nufi da ni ne, meye matsalarki, shin Na'ima "yar ki ce ke kadai, don me za ki tayar mana da hankali, kin hanamu sakat! dan kawai nayi nufin kulla alheri” Ta yi karaf, ta katse shi ta ce "Ka yi niyyar Kulla sharri dai, kuma ba dai da 'Yata ba, banda mugunta, ai ba Na'ima bace kadai 'yarka da ba ta yi aure ba Don me ba za ka canja ba, sai ita, don ba ka Kaunarta." Ya jinjina kai ya ce "Na ji, to meye ya kai ki gidan Halima ki ka yi mata wulakanci? Wannan abin ai tsakanina da ke ne, don me za ki sa yar-uwata a ciki?" Ta ce cike da fusata "Saboda na san duk kulle -kullenta ne wannan saboda ba ta kaunata, shi ya sa take bakin- ciki da kwanciyar hankali na, don haka ka gargadeta ta fita harkata da 'ya'yana". Inna Halima ta dubeta tace. "'Kin ci sa'a a gaban yaya muke, duk abinda za ki fada, ba zan iya maida miki a gabansa ba,