Musabbabi Book 1

Page 23

by @yargidanimam

don yana da daraja da kima a guna." Ta tabe bak; "Wannan ke ki ka sani kuma” Malam Mahmud ya daka mata tsawa ya ce "Ke Hauwa ba ruwanki da Halima kuma idan ki Ka Kara taka gidanta, ki ka yi mata abinda bai kamata ba, sai kin yi mamaki na, don ki sani, ba tsoranki nake ji ba, kin kusa kai ni bango, ki fita a cikin lamarina, kafin na yi miki abinda zakiyi mamaki” shiru ta yi ta na cigaba da kumbure kumbure, Ya bude baki ya kwala ma Na'ima kira. Mama Hauwa ta dube shi ta ce "Wace Na'imar? na riga na turata inda ya kamata, ba kuma za ta dawo ba har sai ka janye wannan mummunar maganar, daka tsiro da ita ana zaune lafiya” 'Malam Mahmud ya fiddo da idanu waje ya ce "Ina ki ka turata ba tare da sanina ko izinina ba?" Ta ce ' ta kara tamke fuska tace “Ba dole bane ka sani, izininka kuwa dama ban nema ba, don na san ba zan samu ba, shi ya sa nayi gaban kaina”, Mallam Mahmud cike da fushi yace “To shikenan ina son ki sani na ba ki daga wannan daran zuwa gobe, ki tabbatar Na'ima ta dawo gidan nan, ko kuma ki tattara ki bi ta , domin bana bukatar ganinki a gidana matukar zansa doka ki ki bi banga amfanin kasancewarki mata ta ba”. Inna Halima tace "A’a yaya kada ayi haka, ka fita harkar Hauwa, don na lura tana jin dadin ci ma mutane mutunci, ka bar ta, duniya ma ai makaranta ce, idan har wani abu zai samu dan wani na assha baki tausaya ba a matsayinki na uwa ba to ba na zaton akwai imani a tare da ke, musaddik kuma da ki ke kyamata ki sani shi ma ba shi ya tsarawa rayuwarsa haka ba, kin kuma fi kiwa sanin cewa da ba haka yake ba, idan baki tausaya masa ba bai kamata ki dinga nuna masa irin wannan tsanar ba” Mama Hauwa ta ce "Kada ma ya bar ni, ba kuma za ta dawo ba, ni ma ba inda zan je, zama daram! Idan kuma neman kwanciyar hankali ku Ke yi to ku janye batun auren nan, shine kawai maslaha, kuma naganar kyamata na kyamace shin meye abin so a gun sa”