Musabbabi Book 1

Page 24

by @yargidanimam

Daga nan ta juya fuuu! Ta shige dakinta gami da rufe kofa. Inna Halima ta juyo tana kallonsa ta ce "Yaya ina ganin maganar Na'ima a bar ta, saboda abinda muke kwadayi, ba za mu samu ba, hakuri da juriyar zama da Musaddik ba za ta iya ba, ko mun tursasa an yi, to ba za mu samu hadin kanta ba balle ta ba mu gudunmuwar dawo da rayuwarsa kan hanya, tunda ba ta so, mahaifiyarta ma ba ta so. Domin tashin hankalin Hauwa ma kadai, ya isa ya hana su zaman .lafiya da kwanciyar hankali, koda ita ma Na'imar tana so. Balle bisa dukkan alamu ya nuna tana tare da mahaifiyarta, tunda har suka iya shirya ta gudu. Allah ya ga tunanin mu, ya kuma ga niyyar mu. Allah ya ba mu ladan niyya, shi kuma Musaddik Allah ya kawo sanadiyyar shiryuwarsa, ko da ba ta dalilin auren ba, domin ko anyi auren sai dai ya kara jefa musaddik cikin wani kangin”. Malam Mahmud ya saki ajiyar zuciya ya ce "Kai babu wata jarabta ga da namiji irin rashin sa'ar mata ta-gari, shi ya sa ba zan taba mantawa da marigayiya ba, wacce ta so-ni, ta yi min biyayya har me rabawa ta rabamu, na yi kwadayin ace ita ce ta cika min gida na da 'ya*ya kafin rasuwarta, amma duk da haka na san tà bar min daya tamkar da dubu wato Afrah" Inna Halima ta gyada kai ta ce "Haka ne, Allah dai ya jikanta, yasa ta huta, tabbas kayi rashin mata” ta karasa magana fuskarta cike da jimami, tana tuna irin zaman arzikin da sukayi da mahaifiyar Afrah. .Mallam Mahmud Ya ture hularsa keya ya ce