Musabbabi Book 1

Page 25

by @yargidanimam

"Amin, kuma ina nan akan bakana na hada Musaddik da 'yata aure” Inna Halima ta dube shi sosai tace “Amma ta yaya, ina za mu iya da tashin hankalin Hauwa, bayan faruwar komai ba ni gaba daya al’amarin ya fita kaina, domin na hango fitina acikin auren nan har garama kada ayi “Mallam Mahmud ya jinjina kai yace “ Na fahimci duk abinda kike nufi na kuma gamsu amma babu komai, akwai wata mafitar da na fara hangowa, bayan maganganun da Hauwa tayi yanzu na hango wata mafitar, ki tashi ki tafi gida dare ya yi sosai, zuwa jibi idan na gama tunani zan neme ki” Ta jinjina kai, ta ce "To Allah ya kai mu, ya kuma kara maka hakuri da juriya akan zama da Hauwa". Ya ce "Amin Halima” Daga nan ta tashi ta yi masa sallama ta leka dakin Afrah wacce duk abinda ke faruwa tana zaune akan katifarta tana jinsu, nan ma sallama ta yi da Afrah. Sannan ta wuce zuwa gida, zuciyarta cike da tsanar Mama Hauwa da jin haushinta.