Musabbabi Book 1

Page 26

by @yargidanimam

Yau alhamis ba makarantar Islamiyya, tun safe Afrah ta kwashe wankin mahaifinta ta wankesu tsaf? Ta shanya; sannan ta shiga dakinsa ta gyara Kamar yadda ta saba duk ranar alhamis, haka zalika duk wani aikin gida, babu wanda Mama Hauwa ba ta, ba ta ba, duk kuma ta yi ta gama har zuwa yanzu da ta hada wutar guga ta goge kayan mahaifinta Ta kammala kenan, ta kwasa za ta kai masa daki, ya dawo, ya shigo yana kallonta dauke da kaya ya ce "Afrah, yanzu bayan wanki har guga Ki ka sami damar yi min, bayan aikin da na fita na bar ki da shi a gaba?" Ta yi murmushi ta ce "Eh Baba, ai har ma na gama, sannu da zuwa" cike da kauna yace “ Yauwa Allah miki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah ya baki kema masu jin kan ki, masu taimakon ki yadda ki ke taimako na”. Cike da jindadin addu’ar tace “Amun Baba” Daga can nesa inda Mama Hauwa ke zaune ta saki tsaki ta ce “ Ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta”, wani irin mugun kallo ya sakar mata sannan ya wuce dakinsa ba tare da ya tanka mata ba, don maganar gaskiya haushi take ba shi ba ta ko son kallonta. "Ayi dai mu gani." Ya yi mata wani irin Ita ma Afrah ta bi bayansa dauke da kayan a hannunta. Tana shiga dakin ta tarar da Malam Mahmud zaune akan kujerar da ita kadai ce a dakin, ya yi tagumi hannu biyu fuskarsa dauke da matsananciyar damuwa, bayan ta aje kayan ne,inda ta saba ajewa ta shiryasu, sannan ta