Musabbabi Book 1

Page 27

by @yargidanimam

juyo ta dora masa ido, zuciyarta ta dagule ta shiga damuwa, domin gain mahaifinta cikin damuwa. Tana matukar so ta zauna su tattauna damuwarsa, amma ba ta da yadda za ta yi, domin bai nemi hakan daga gareta ba, ta juya a hankali zata fita, har ta kai kofar dakin, zuciyarta cike da addu’ar Allah yasa ya kirata domin su tattauna damuwarsa, ta ji muryar mahaifinta ta dakatar da ita daga fita, ta hanyar kiran sunanta, ta amsa da sauri, lokaci daya ta dawo ta durkusa a gabansa ta ce "Ga-ni Baba” Malam Mahmud ya dawo da kallonsa gareta, ya fara magana. "Afrah ina cikin wani hali na tsaka mai wuya, na daukar ma kaina alkawarin da na ke neman na gaza a kansa, na shiga wani hali da banda wani zabi da ya wuce na roke ki a matsayinki na wacce na ke tunanin tana da maganin matsalata." Ya dan numfasa, sannan ya ci-gaba da cewa "Musaddik Dan-uwanki ne, idan rayuwarsa ta gyaru, na yi imanin za ki zama daya daga cikin masu jin dadì, ko kadan ba ni da nufin kara ma rayuwarki damuwa, saboda maraicin ki da kuma irin hannun rikon da ki ka taso. Hakan ya sa na ke miki kwadayin samun miji na-gari wanda zai taimakeki, wanda zai rikeki da mutunci, wanda kuma za ki sami dukkan gata daga gare shi Shi ya sa ban yi tunanin hadaki aure da Musaddik ba, don na san duk abinda na lissafa,