Page 28
ba za ki taba samu daga Musaddik ba, shi ya sa na yi tunanin hada shi da "Yar-uwarki Na'ima.” Ya numfasa gami da gyara zamansa, ya kurama fuskar Afrah ido wacce take tsugunne, banda faduwar gaba ba abinda take yi, ya ci-gaba da cewa “Ba sai na gaya miki matsalar da na ke fuskanta daga Hauwa ba Tunda na furta maganar hada auran nasu, domin na san kin ji, kin kuma ga irin cin mutuncin da Hauwa ke min, karshe ma ta dauke Na'ima ta boyeta, ban san inda ta kai ta ba. Don haka Afrah ina rokonki da hannaye na biyu, ki taimakeni ki share min hawaye, ki sadaukar da farin-cikinki saboda farin-ciki na, ki yi min biyayya kamar yadda ki ka saba, ki amince ki auri Musaddik don Allah... Da sauri Afrah ta dakatar da shi "Don Allah Baba ka daina rokona, wace ce ni da har sai ka rokeni, don na yi maka biyayya, duk irin so da kauna da ka nuna min ace sai ka rokeni don kawai za ka aura min Dan-uwana. Har kullum ina fatan Allah ya kawo ranar da za ka nemi wani abu daga gareni, domin ba ni da abinda zan saka maka ko na biyaka daga irin rikon da ka yi min “ Ta yi kokarin maida hawayen daya cika mata ido, sannan ta ci-gaba da cewa "Saboda haka zan sadaukar da farin-ciki na, kamar yadda ka