Page 29
bukata, zan auri Yaya Musaddik, zan kula da shi tare da kokarin sanya shi a hanya madaidaiciya Allah kuma ya shirya shi." Son Afrah tare da tausayinta ya kara kama Malam Mahmud, a yayin da farin-ciki ya cika zuciyarsa, amma daya kalli cikin idanun Afrah, sai ya ji wani bakin-ciki ya kama shi, domin duk yadda Afrah ta so ta Boye damuwarta, to ba za 6oye ma Malam Mahmud ba, hakika bai hango son Musaddik ko son auransa a kwayar idanunta ba. Abinda ya hango daya ne, shi ne tsantsar biyayya da kaunar faranta ransa, ya nisa gami jinjina kansa sannan ya ce. "Ki yi hakuri Afrah, ba haka na so rayuwar ta tafi ba. Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki 'ya"ya masu jinkanki, Allah kuma ya albarkaci abinda zai shigo rayuwarki. Allah ya juya wannan al'amari ya kasance alheri a gareki, da mu ba ki daya, domin Allah ya ga kyakkyawar niyyar mu akan wannan auran, na gode, na gode" Afrah ta dan yi murmushi ta ce “ Baba kana sa ni jin nauyi, idan ka na min godiya, don Allah Ka daina min godiya". Ya gyada kai cike da kauna yace “Allah ya yi miki albarka Afrah tashi ki tafi.”. ' A hankali ta mike ta fita, gabanta na cigaba da matsanancin faduwa. Tana shiga dakinta ta fada kan katifarta,kuka take riris Komai ya kwance mata, meke shirin faruwa da ita? Ko a mafarki ba ta taba kwatanta