Page 30
Musaddik a matsayin mijin aurenta ba, shin me kaddara ta tanadar mata? Zama da mutum irin Musaddik wanda bai ma san inda rayuwarsa tasa gaba ba. Wanda bai san yadda zai tarbiyantar da ita ba sai dai ita ta tarbiyyar da shi, ko kadan ba irin Musaddik bane mijin da take kwadayin zama a karkashinsa. Ya Sayyadi Habib shine wanda ta horar ma da zuciyarta kaunarsa, take kuma kwadaita ma kanta auransa. Domin tana da tabbacin shine wanda zai yi mata jagora har gidan aljanna, sai dai kash! Ba ta so yadda labarin ya tsaya ba, ba ta so karshen labarin ya zama haka ba. Domin kuwa ko ta ki ko ta so soyayyarta da Ya Sayyadi ta zama tarihi daga lokacin da mahaifinta ya umarceta da auran Musaddik, tabbas! Za ta yi ma mahaifinta biyayya, koda hakan zai zama sanadiyyar fadawarta mummunar rayuwa, domin duk duniya ba ta da kamar mahaifinta. Ba ta tunanin akwai abinda zai bukata ta yi masa, matukar tana da halin yi masa ta kasa yi, don haka za ta iya sadaukar da komai nata, domin samun farin-cikin mahaifinta, tunda Allah ya taimaketa ta samu ta yi rayuwa da shi, dole ta lallaba ta samu albarkansa, tunda Allah bai kaddari za ta yi rayuwa da mahaifiyarta ba. Ta sa hannu ta goge hawayen da ke malala a saman kumatunta, ko kadan babu soyayyar Yaya Musaddik a cikin zuciyarta.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam ✍️
Kuyi comments da ra’ayiyun ku rashin yin comments zai iya sa wa na daina posting MUSABBI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM