Musabbabi Book 1

Page 31

by @yargidanimam

sai dai acan karkashin zuciyarta akwai tsantsar tausayinsa, gefe daya kuma tana tausayin kanta da Ya Sayyadinta na yadda za su rabu da junansu, domin Allah bai rubuta shi ne mijinta ba a allon kaddarar su, ta kara goge hawayenta. Sannan ta yunkura ta tashi ta tura kofar dakinta, domin ta ji dadin yin kukanta, sannan ta dawo ta kure karshen katifa ta ci-gaba da rasgar kuka,; domin tana ganin hakan ne kawai zai sassauta mata radadin da take ji a cikin zuciyarta. Haka Afrah ta kasance cikin rashin sukuni a wannan ranar, har zuwa idar da sallar Issha'i, tun bayan idar da sallar, tana zaune akan sallaya da casbaha a hannu tana lazimi, lokaci daya ta kan yi kokarin goge hawayen da ke fita mata da daya hannun. Tana jin dawowar mahaifinta daga masallaci, bai dade da shigowa ba, kuma ta ji sallamar Inna Halima, haka nan Afrah ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba. An dau tsawon lokaci kafin ta ji muryar Malam Mahmud, ya kwala mata kira. A daburce ta amsa da sauri, ta tashi ta aje carbin, sannan ta fice kai tsaye dakin mahaifinta ta nufa. •Mama Hauwa da ke zaune a kofar dakinta ta rakata da kallo har ta shige dakin, sannan ta saki tsaki ta tashi ta dauki kujerarta 'yar tsugunne ta