Page 32
shige daki tana fadin "Halima uwar kinibibi, sai dai ya Kare a kanku ba dai 'yata ba”, a fili take fadan maganar cike da zafin rai. Cikin sallama Afrah ta shiga dakin, ta yi Kokarin boye dukkan damuwarta, ta nufi inda Inna Halima ke zaune, ta zauna kusa da ita. "Inna sannu da zuwa” Ta amsa tana yi mata wani kallo me cike da Kauna da tausayi, ta fara magana "Afrah ban Yarda da hukuncin da mahaifinki ya yanke ba a Kan aurar dake ga Musaddik. Afrah ke marainiya ce ina matukar tausayin rayuwarki, miji irin Musaddik bai kamace ki ba, gara kawai an hakura mu ci-gaba da yi masa addu'a." Afrah ta yi dan murmushi gami da kallon Malam Mahmud, wanda ya yi tagumi hannu biyu, sannan ta dawo da kallonta ga Inna Halima ta ce "Me ya sa za ki fadì haka Inna? Ya za ki ce miji irin yaya Musaddik bai dace da ni ba, bayan jininmu daya. Dan-uwana ne, käda fa ki manta a da, ba haka rayuwarsa take ba, ina ganin kuma kuna son ya yi aure ne, saboda ya samu natsuwa. To ai ina ganin wannan jahadi ne gaba dayan mu lada za mu samu, kuma akan maganar yi ma mahaifina biyayya, ina miki rantsuwa ko wuta ya hura ya ce na fada, zan fada;, domin da 'shi kadai na samu nasara yin rayuwa, bayan Allah ya amshi ran mahaifiyata, don haka ina so ki sa a ranki, auran