Musabbabi Book 1

Page 33

by @yargidanimam

Yaya Musaddik shine biyayya mafi kankanta da na ke ganin zan iya yi ma, mahaifina. Hawaye ya digo a idanun Inna Halima, so da Kaunar Afrah ya kara kamata, ta dubi Malam Mahmud wanda shi ma maganganun Afrah sun taba masa zuciya, ido kawai ya dora mata, yana yi ma Allah godiya a zuciyarsa daya ba shi "ya irin Afrah.Inna Halima tace '"Gaskiya ne yaya. Allah ya ba ka 'ya daya tamkar da dubu, yau Afrah ta sa ni alfahari da ita, ta Kara dasa min soyayyarta, zahirii mun yi dace da samun ya irin Afrah. Me cike da tausayi, jinkai da uwa uba ilimin addini daya gama ratsa zuciya da jikinta, hakika Musaddik mun yi masa dukkan gata, na ba shi mata irin Afrah, ina kuma da tabbacin Afrah ita ce sanadiyyar maido da shi irin hanyar da yake akai a da, ba ni da haufin itace zata taimaki rayuwar Musaddik” tasa hannu ta kara jawo Afrah cikin jikinta ta rungumeta sosai tana fadin "Allah ya yi miki albarka , Allah ya hadaki da dukkan farin-ciki a gidan Musaddik da rayuwarki duka, ke ma Allah ya ba ki ya ya irin ki masu biyayya”

Malam Mahmud ya amsa da "Amin Halima, ai Afrah ta zama sanyin idaniyata, ta, zama farin ciki na, darajarta da kima sun kara fadada a zuciyata, ba ni da kamarta a duk 'ya yan da na haifa. Matsayinta daban yake"