Musabbabi Book 1

Page 34

by @yargidanimam

Inna Halima ta ce “Tabbas hakane yaya” Kalaman Malam Mahmud sun sanyaya zuciyar Afrah daga kunci, natsuwa ta fara zuwa mata, ta kuma kara dammarar amincewa tare da yarda da umarnin mahaifinta. Malam Mahmud ya ce. "Halima ki nemi Musaddik gobe ki yi masa bayanin canjin alherin da aka samu, ya zo su yi magana da Afrah, domin auransu ba na so ya wuce nan da wata daya” Gaban Afrah ya fadì, ta runtse idanunta ta bude. Wata daya! Da sauri ta tashi daga jikin Inna Halima ta fice. Inna Halima ta bi ta da kallo tana murmushi tace “ kunya ki ke ji Afrah?”, ta gyara zama Ta dawo da kallonta ga yayanta tace "Eh, to ai daukar lokaci baida wani amfani, tunda dama Islamiyya ce kawai take zuwa, aure kuma ba zai hanata zuwa da kuma koyar da dalibanta ba, saboda hakan goben nan zan kira shi na san kuma duk inda yake zai amsa kirana da gaggawa, don ko a wane hali yake baya iya kin amsa kirana, ko da zai shigo min acikin yanayin da zan uni zubar da hawaye”. Yace

"To shi kenan. Allah ya kai mu. Ita kuma Hauwa sai ta jika Na'imarta ta sha". Inna Halima ta ce "Lallai kam! Shi ya sa ai aka ce gida biyu, maganin gobara, yau da Na'ima ce kadai 'yarka da bakin-ciki ya kashemu, taje ta zaba mata wanda ya fi kowa natsuwa a duniya, to wai yaya idan ana kyamatar irin su musaddik ta yaya zasu shiryu”, ya jinjina kai yace “kwarai Halima irin su janyosu ake ajiki a nuna musu souayya da tausayi sai kiga idan da rabo wata rana mutum ya daina ya shiryu, yanzu idan Hauwa ce ta haife shi zata kyamace shi ne irinsu ma iyayensu mata sun fi son su, Allah dai ya shiryi Hauwa domin in da zata daure data da gyara da yawa da yakamata ta zauna ta gyara”, inna Halima tace “ Allah dai ya shiryeta”, Mallam Mahmud ya kalli agogonsa dake manne a jikin bangon dakin, sannan ya dawo da kallonsa gareta yace “Dare ya yi Halima ki tashi ki tafi gida kada Mai-gidan ya ga dadewarki".ta tattaro hijabinta tace "To Allah ya tabbatar mana da alheri" Ta tashi ta