Musabbabi Book 1

Page 35

by @yargidanimam

gyara zaman hijabinta, sannan ta yi masa Sallama ta fita zuwa dakin Afrah, amma sai ta ta tadda ta tana shafa'"i da wutri, don haka ta wuce zuwa gida zuciyarta fes! Da farin-ciki Afrah ta share masu hawaye

Washegari tun safe Inna Halima ta kira Musaddik a waya, don haka gab! Da azahar ya shigo gidan idanunsa jajir! Kayan jikinsa kuwa kaca-kaca duk sun dafe da datti, kai da gani ka san sun dade a jikinsa, sai da Inna Halima ta samu natsuwarsa, sannan ta gaya masa duk halin da ake ciki a yanzu. Musaddik ya yi shiru, jikinsa ya yi matukar sanyi a hankali ya ce "Afrah Inna?"ta gyada kai tace "Ita fa". Ya girgiza kansa ya ce "A gaskiya Inna ba"a yi ma Afrah adalci ba. Matukar aka aura mata ni, domin ta kowace fuska ba mu dace ba, tana da hankali, tana da natsuwa tana da kunya, uwa uba tana da matukar riko da addini, ya kike ganin mai irin wannan halin ta dace da ni, da banda aiki sai zubar da mutunci” Inna Halima ta kafe shi da ido tana ganin yadda duk ya birkice da ga jin maganar , ta aje numfashi tace "Kada ka damu ko kadan dama wadannan halayen na ta da ka fada sune dakilin hada auran naku, domin za mu hada ka aure da ita ne domin muna da tabbacin da wadannan halayen da ka lissafa zatayi amfani da su za ta janyo hankalinka, ka natsu ka zama mutumin kirki kamar da, don haka wannan babbar dama ce a gareka, damar da nake da tabbacin ba zaka kara samun ita ba”