Musabbabi Book 1

Page 36

by @yargidanimam

Musaddik ya dago ya dubeta ya ce idanunta sun kara rinewa yace “ Amma Inna, takurawa Afrah kawai ku kayi ta aure ni, ba don wai tana sona ba, idan kuma hakane gaskiya inna ba dai dai bane” Inna Halima ta girgiza kai ta ce. "Kada ka sa ma kanka dole sai ka gano tana sonka ko ba ta sonka, abu dai mafi dadi, shi ne da kanta tà amince za ta aureka, don haka duk ka aje wannan kwakule-kwakulen ka yi ma Allah godiya daya ni'imtaka da samun Afrah. Kawunka kuma ya umarce ka da ka je ku tattauna da ita" Ya Kara kallonta ba tare da ya yi magana ba, ta ci-gaba da cewa "Eh, saboda auran ba zai wuce nan da wata daya ba” "Wata daya?" Ya tambaya a gaggauce tace

"Eh, wata daya. Ko akwai wani abin ne?" Ya girgiza kansa ya ce "Babu komai Inna, zan yi kokari naje, nagode Allah ya saka maku da alheri, ya kuma baku ladan zumunci, domin babu abinda zance da ku ina ganin halaccin dangin uwa” tayi murmushi Tace “Amin, sai dai kada ka je mata a haka, ko yaya ne ka samu kaya masu tsafta kasa idan za ka je, kuma ka tabbatar kana cikin nutsuwarka don Allah musaddik kada ka sha komai “ musaddik ya yi kasa da idonsa Ya dubi kayan jikinsa, shi kansa ya san ya yi datti, ya yi dan murmushi sannan ya ce "To Inna nagode zan kiyaye”. Daga nan ya tashi ya tafi, haka nan ya ji ya sami kansa da jin wani farin-ciki, hakika samun Afrah a gare shi ba karamin al'amari bane, duk da babu son aure a zuciyarsa. To fa, sai ya ji ya samu kansa da jin dokin son auran Afrah wacce ko a mafarki bai taba lissafota