Page 37
a cikin matan da zai aura ba, duk da rayuwarta ta dade tana burge shi, tana daya daga cikin mutanen da yake jin nauyin aikata mummunan abu a gabansu, shi kansa bai san dalili ba. Amma ya san dai yana matukar jin nauyinta duk da kananan shekarunta.
Yau kwata-kwata a makaranta Afrah ta kasa samun natsuwar da za ta koyar da dalibanta, tana cikin matukar damuwa wacce iya yadda ta so ta boye, sai da Sayyadi Habib ya fahimci tana cikin damuwa, saboda haka bayan an tashi, suna kan hanyarsu na zuwa gida ya dan dubeta cikin nazarin yanayinta yace “Afrah me ke faruwa ne?”, ta dan dube shi tace “ me ka gani?”, ya yi murmushi yace “kin tabbata cikakkiyar yar nigeria me amsa tambaya da tambaya”, ta kara murmusawa tace “ai ban fahimceka bane shi yasa na tambaya” yace “Ni kuma na fahimci damuwar dabkike ciki shi yasa na tambayeki “ Ta girgiza kai ta ce “Ba ni da wata damuwa “
Ta fada a gajarce, ya girgiza kai Ya ce "Ki na da ita, sai dai idan ki na kokarin Boye min, wanda ina ganin bai kamata ba, duk da ban san damuwar ba, na san idan ki ka gaya min zan amfaneki koda da shawara ne ko nasiha, amma idan ki na ganin sanina bai zama dole ba, to ki bar shi ba sai kin gaya min ba, na dinga taya ki da addu'ar Allah ya kawo miki mafita.”