Page 38
Nan da nan idanunta suka cika da kwalla , ta yi kokarin maidawa sannan ta ce "'Hakika idan akwai wanda ya cancanci ya san damuwata a yanzu, to kai ne, domin damuwar ba tawa bace ni kadai, ta mu ce mu duka Ya kalleta, nan da nan ya ji damuwa ta cika ransa domin ganin yanayin davta koma . Yace “To idan har haka ne, me ya sa ba za ki gaya min ba, ko don mu hadu mu shawo kan matsalar gaba daya" ta aje ajiyar zuciya tace "Hanyar da zan bi na gaya maka ita ce na rasa, domin ban san yadda za ka dauki lamarin ba” ya girgiza kai yace "Zan dauke shi a duk yadda ya zo min, domin Allah ya fi ni sanin dalilin yin komai" Ta numfasa dai-dai lokacin da suka iso kofar gidansu, suka tsaya sannan ta ce "to shi kenan kayi hakuri zuwa gobe, za mu yi magana, zan sanar da kai komai, sai dai, ina addu'a tare da fatan Allah ya ka fahimce ni” Ya yi dan murmushi ya ce “ Bazan tursasa miki ki gaya min yanzu ba, zan jira har zuwa goben, sannan ina tabbatar miki da cewa zan fahimceki, domin na san halinki gaba da baya" Ta gyada kai ta ce "To na gode: Ya Sayyadi, Sai goben” ya gyada kai yace “Allah ya kai mu, ki gaida mutan gidan” tace “ zasu ji n sha Allah “ Daga nan ya tafi, zuciyarsa cike da sake-sake akan damuwar Afrah, wacce ya ji