Page 39
tun kafin ya san damuwarta ta shi ma damuwar ta kama shi .Afrah na shiga gdan ta yi turus a sakamakon ganin Musaddik tare da mahaifinta a zaune akan tabarma . Tayi saurin kallon kofar dakin mama Hauwa ta ganta a kulle alamar bata nan , don haka ta karasa shigawa gidan tana kokarin kauda duk wata damuwa da ke tare da da ita. “ Afrah an dawo?” Cewar mahaifinta, ta gyada kai fuska sake tamkar ba ta cikin damuwa ta ce “ Na dawo Baba, sannu”, musaddik ya dago Ya dubeta zai yi magana kenan, ta riga shi "Sannu da zuwa yaya" Ya kara dagowa sosai yana cigaba da kallonta sosai, duk da hakanan take masa kwarjini sai ya ji duk ya na neman ya rikice. a sanyaye yace
“ yauwa sannu ya makarantar?"ta kara yin murmushi tace “ lafiya kalau” Cike da farin-ciki Malam Mahmud ya ce "Tun dazu ya zo gunki, bai san ki na koyar da dalibai ba a irin wadannan ranakun, ganin kin kusa dawowa, ya sa na tsayar da shi akan ya jiraki". Ta gyada kai tace “ To baba bari na shiga daki na aje littafaina” mallam mahmud ya dubi musaddik ' Ya ce "Ba damuwa zai sameki a dakin”
Ta wuce da sauri zuwa daki, ta kintsa kayanta da ta bari kan katifa, ba•ta cire hijabin ba, nikaf kawai ta cire ta nemi bakin katifar ta zauna ta takure gu daya, lokacin daya kuma tana karanta "Inna-Lillahi' wa-Inna Ilaihir-Raji'un! Domin ta samu natsuwar zuciyarta, domin ko kadan ba ta son