Page 40
Musaddik, yav fahimci tana cikin damuwa akan. auransa Cikin sallama Musaddik ya shigo dakin, ta amsa masa lokaci daya ya sami kan tabarmar dake shimfide a tsakar dakin ya zauna yana Kallonta a hankali ta gaishe shi, ya amsa, sun dau tsawon lokaci ba tar da ya iya yin magana ba daga bisani ya numfasa ya ce. "Afrah ki na gain maganar auran mu babu cutarwa a bangaren ki?" Yayi tambayar ne cikin wata murya ne cike da gazawa, Ta daidaita muryarta ta ce "Cutarwa? Wane irin cutarwa?" Ya muskuta yace "Ni ina ganin kamar babu dacewa a tsakanin mu Afrah, halina ba Boyayye bane, rana tsaka na sami mugun canjin rayuwa Irin rayuwar da na ke yi a yanzu na fi kowa tsanar irinta a da, amma ban san kaddarar da Allah ya Kaddara min ba, na sami kaina a rayuwar da na tsana, ki na ganin za ki iya zaman aure da mutum irina me shaye-shaye da gurbatacciyar rayuwa, domin kinsan komai ba kuma na son boye miki komai, sannan bansan dalilin da yasa na ji ba na son ji dunga samun damuwa ta dalilina , ina jin kamar bazan iya jurewa ba” Afrah ta runtse idonta ta bude, zuciyarta ta Kara cika da tashin hankali gami da tausayin musaddik ta ce "Zan iya auranka mana, zan iya zama da kai koda halin da ka ke ciki ya fi haka munana, domin ina da tabbacin wata rana zaka daina, za ka shiryu don na san wannan ba rayuwarka bace a da”. Sha'awar halayenta da natsuwarta suka kara kama musaddik ya kara zuba mata ido .
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan umam
Kuyi commitments domin gujewa rashin cigaban zuwan sauran posting. MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM