Musabbabi Book 1

page 41

by @yargidanimam

Yace “ Amma kin zauna kinyi nazari akan rayuwata da makomar aurena” ta muskuta gami da yin wani dan takaitaccen murmushi sannan tace,”idan aka zo maganar biyayyar mahaifina bana tunanin komai sai alheri saboda haka alheri kawai na zauna na hangoma kaina agame da aurenka,kuma na amince zan aureka”. Wanna kalamai sun fi komai dadi a zuciyar Musaddik, ya aje numfashi gami da kallonta Sannan yace “Wanda na ganku tare ranar da na zo wajen Na’ima meye matsayinsa a gunki?" Tsigar jikinta ta tashi, damuwa ta kara cika zuciyarta, kallon da ya tsareta da shine, ya sa jikinta ya yi matukar sanyi, ta ji kuma ba za ta iya gaya masa gaskiya akan Ya Sayyadinta ba, domin ba ta ga amfanin hakan ba, tunda ta riga ta zabe shi a matsayin mijinta. Ta kwakulo murmushi gami da gyara zamanta sannan ta ce "Matsayi kuma? Ba komai tsakanina da shi daya wuce Malami na, ni dalibarsa ce". ya lumshe idanunsa ya rasa dalilin da yasa ya ji matukar dadi da jin amsarta ya ce. "Ki na nufin ba ki da wani da ki ke soyayya da shi, kada na zama sanadin datse soyayyar?" Ta girgiza kai ta ce "Ba ni da kowa, ina son kuma mu bar maganar nan"cikin murmushi yace "An gama ranki ya dade” Ta dan yi murmushi ta ce “Na ji Baba na maganar ba za'afi wata daya ba za’a daura auren ko?” Musaddik ya gyara zamansa yace "Eh, haka ya yi min bayani dazu, domin har ya ba ni damar ma na je na gaya ma Hajiya cewar ya ba ni ke, ya sa kuma ramar biki wata daya me zuwa, wato uku ga watan da zai kama kenan”.