Page 42
'Nan da nan Afrah ta ji ta kara gigicewa, bakinta ya shiga karanta “Allahumma ajirni fi musibati wa akalifni khairan minha” amma a cikin zuciyarta a fili kuwa ajiyar zuciya ta saki tace “To Allah nuna mana” ya datseta da ido yace “ko akwai wani abu ne Afrah, don Allah duk abinda ke ranki ki fito ki gaya min kada ki damu ina tare da ke” Ta girgiza kai tace “ Haba yaya musaddik babu wani abu fa,kawai dama ina son na rokeka ne ko bayan munyi aure zan cigaba da zuwa islaniyya, zan kuma cigaba da koyar da dalibaina” Ya yi murmushi ya ce “ kada ki damu zaki cigaba da zuwa islamiyya, meye ribata idan na hanaki zuwa makaranta, duk abinda kike so ni ma ina Ta yi dan murmushi tace “ To nagode” ya girgiza kai yace “ Ni ne da godiya Afrah ba kuma zan taba mantawa da wannan halaccin ba”.
Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa, kai ka rantse da Allah Afrah tana son Musaddik, kuma tana son auran. Shi kuwa haka nan ya ji matukar natsuwa a dalilin hira da ya yi da ita, har zuwa lokacin da aka kira sallar magariba, sannan ya yi sallama da ita, ya fita tare suka yi alwala. da Malam Mahmud. gwanin ban sha’awa kamar ya dore a haka sannan Suka tafi masallaci, duk da ko azahar bai yi ba balle la'asar, amma ya zai yi, tunda Malam Mahmud ya sa shi a gaba zuwa masallacin.