Musabbabi Book 1

Page 43

by @yargidanimam

Washogari kuwa cike da fargaba Afrah taje makaranta, haka zalika har aka tashi makaranta Islamiyyar Afrah ta kasa hada ido da Ya Sayyadi Habib, haka zalika damuwarta ta fi ta ko yaushe fitowa. Saboda tasan ya zama dole dai yau ta sanar da shi komai . A cikin ajin makarantar suka kasance, baya an tashi kowa kuma ya watse, a natse Ya Sayyadi ya dubi Afrah ya ce. "Fateema, damuwa ba ta maganin damuwa haka zalika duk abinda ya shigo rayuwar bawa, hakuri ya kamata ya runguma gami da addu'a saboda haka ina son ki natsu ki yi min bayanin abinda ke faruwa, ko akwai ta inda zan iya taimakawa kamar yadda na fada miki” Afrah ta numfasa gami da gyara zaman nikaf dinta a fuska, sannan ta fara magana a hankali “Ya Sayyadi, da farko dai ina son ka sani, ka Kuma sa a ranka kai ne da namiji na farko da zuciyata ta fara so Ta kuma yarda da ta zama abokiyar rayuwarka, domin ina da tabbacin kai ne wanda Zaka yi min jagora zuwa gidan aljanna da Kyakkyawan halayenka da kuma iliminka me guda na Ba na hangen komai ko kwadayin. komai daya wuce na san za ka sanyani a hanyar bin dokokin Ubangiji wanda shine burina” Ta dan numfasa tana kallonsa. ganin bai da alamar yin magana ya sa ta cigaba da cewa.