Page 44
"Sai dai kash! Komai Allah ya riga ya gama tsarawa, ba mu da yadda za mu yi, sai yadda ya yi da mu, kaddara ba ta rubutaka a matsayin mijin aurena ba” a gaggauce ya dago ya dora mata furgitattun idanunsa da suka rikide nan da nan suka yi jajir! "Kamar yaya?" Ya Sayyadi ya yi gaggawar tambaya, ta jinjina kai sannu a hankali ta kwashe labarin komai ta sanar da shi. Ta kara da cewa "Allah shine shaida, ko kadan ba na son Yaya Musaddik, ban taba son sa ba , bai taba burgeni ba, haka zalika ban taba yi ma kaina sha'awar auransa ba, don na san babu wani alheri da zan samu a cikin. auransa Amma abu daya na daukar ma kaina, shi ne yi ma mahaifina biyayya a cikin duk wani abu da bai saba ma umarnin Ubangiji ba, zan yi ma mahaifina biyayya koda yin hakan zai kuntata ma rayuwata, zai kuma kori farin-ciki na matukar mahaifina zai yi farinciki To a shirye na ke da na yi komai, saboda haka ina mai ba ka hakuri, kai na ke so, amma Yaya Musaddik zan aura, domin cika umarnin mahaifina, ka yi hakuri Ya Sayyadi, ka yi min afuwa." Ga tsananin mamakin, Afrah, sai, ta ga Ya Sayyadi ya yi wani bushashshén murmushi, Sannan ya numfasa ya dauki wani dogon lokaci Yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, har ta gaji ta