Musabbabi Book 1

Page 45

by @yargidanimam

domin ta kosa kwarai ya ce wani abu, sannan daga bisani ya fara magana cikin sayin jiki da sanyin murya. '"A yau na kara yin alfahari da ke, hakika ke yarinya ce me tsananin hangen nesa, tunaninki Ya yi nisa da shekarunki, komai na rayuwarki abin burgewa ne, ki na daya daga cikin 'ya 'yan da iyaye suke alfahari da su." Kalamansa sun sa Afrah ta fara samun natsuwar zuciyarta, ya ci-gaba da magana, “Ban ji haushin biyayyar da za ki ma mahaifinki ba, hakan ma ya Kara sa min sonki da sha'awar halayenki ne, ya kuma Kara miki wani matsayi na musamman a zuciyata, kin kuma zama abar kwatanta halayenta a wajen duk wani mai hankali. Sai dai ina taya kaina jimami da alhinin rabuwa da mace irinki, domin ke ce irin uwar da Manzon rahama ya umarcemu da mu zaba ma Yayan mu , na yi mafarkin kasancewa da ke a matsayin matata uwar 'ya 'yana, wacce za ta yi ma ya'yana tarbiyya, amma Allah bai nufa ba, b bazan ji haushi akan kaddararsa ba. Domin yarda da kaddara mummuna da kyakyawa, cikar imani ne, na kuma yarda da kaddara a matsayina na masulmi, sannan babsan irin tanadin sa Allah zai yi min ba akan hakurin da na yi”.

Ya nisa ya ci-gaba da cewa "Ba zan so kaina na ce kada ki yi ma mahaifinki biyayya ba, haka zalika Musaddik ya fi bukatar ki fiye da ni, domin