Page 46
shi yake bukatar nasiha tare da dora shi a hanya Kuma dole na so masa abinda na ke so ma kaina, domin imanin dayanmu baya cika, har sai mun soma Dan-uwanmu abinda muke so; ma kanmu. Saboda haka ki ciré damuwa a zuciyarki, zan goya miki baya dari bisa dari har sai kin cimma burinki , nasan ahankali damuwa zata sake ni”. Murmushi ya subuce a fuskar Afrah, ta kura ma Ya Sayyadi ido, hakika kallo daya za ka yi masa, ka san yana cikin matsananciyar damuwa amma baya son bayyanawa. Hakika Ya Sayyadinta ya cika gwarzon maza, ya cika jarumi. Jarumi , ta nisa tace “Hakika Ya Sayyadi ban taba ganin namiji me zuciyar imani da tausayi da kuma fahimta Irinka ba, tabbas ina taya kaina jaje da bakin-cikin rashin masoyi irin ka, sai dai tarihin rayuwata na san ba zai taba kammala ba, ba tare da ka shigo ciki ba bazan taba mantawa da kai ba har na koma ga mahaliccina”.
Ya jinjina kai yana kokarin maida hawayen da ya taru masa a ido, ya ce "Babu komai, Fateema haka Allah ya tsara mana, ba kuma za mu taba yin fushi da yinsa ba, domin ya yi mana ni’imomi da yawa , don ya hanamu abu daya bai Kamata mu sa damuwa ba, bayan ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya yi hakan”.