Musabbabi Book 1

Page 47

by @yargidanimam

Ita ma ta sa hannu kasan nikaf dinta ta goge hawayen da ke fito mata, sannan tace “Ina neman alfarma daya daga gareka Ya Sayyadi." Ya dago ya dubeta ya ce "Wace irin alfarma ce? Tace "Ina neman alfarmar ka zama yayana. wanda zan nufo shi a duk lokacin da na ke bukatar taimako, ina son ka ci-gaba da kasancewa malamina wanda zai dinga yi min nasiha a duk lokacin da zan kauce hanya, ina son ka kasance Me karfafa min guiwa mashawarcina a cikin Wannan sabuwar rayuwar da zan shiga, wacce ban san daga inda zan farata ba”, Ya Sayyadi Habib ya goge hawayen da suka ziraro masa, ya yi saurin juya bayansa, domin ko kadan baya son ta fahimci damuwarsa ta, tsananta, baisan ya karyar mata da guiwa yace "Kada ki damu, duk a yadda ki ke son na kasance miki zan kasance, na yi alkawarin zama yayanki kuma malaminki, har karshen rayuwata, duk abinda yaya yake ma kanwarsa, na yi alkawarin zan yi miki, ke ma kuma ina rokon alkawari daya daga gareki" Afrah ta ce "Me ka ke so Ya Sayyadi?" Ya ce ba tare da ya juyo ba "Ina son ki yi min alkawarn ba za ki daina neman ilimi ba, ba kuma za ki daina koyar da dalibanki ba, za kuma ki kasance mai hakuri da juriya a cikin wannan auran naki."