Page 48
Afrah ta kara goge hawayenta ta ce “ Nayi maka alkawari Ya Sayyadi, na yi maka in sha Allah”, daganan ya juya ya dubeta yace “Ta shi ki tafi gida”, tayi masa wani irin kallo me cike da tausayawa, tace “Na yi zaton tare zamu tafi kamar yadda muka saba”, ya girgiza kai yace “kada ki manta yanzu a matsayin yayanki nake ba me neman aurenki ba, saboda haka ki tafi zan taho daga baya”. Ta gyada kai ta so su cigaba da magana amma kiran sallar magriba ya sa tayi saurin yi masa sallama ta fice a sanyaye.
Ayayin da ya sayyadi ya koma kan kujerar ajin ya zauna yayi tagumi hannu bibiyu, komai ya tsaya Masa cak bai taba zaton haka lamarin zai tsaya ba Allah ya sani ya yi, bakin-ciki na rabuwa da Afrah, domin da ita ya yi mafarkin gina rayuwarsa, zuciyarsa ta yi kuna, ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dadi, yana son Afrah matuka, amma dole ya goya mata baya, domin zama cikakken masoyinta.