Page 49
Bayan sallar Issha'"i. Mansur da Kabir suka shigo gidan domin amsa kiran mahaifinsu, duk suna zaune akan tabarma a kofar dakin Mallam Mahmud. Mama Hauwa na zaune akan kujera yar tsugunno tana jin maganar da Mallam Mahmud yake yi “Duk kokarina na hada Na'ima da Musaddik aure, abin ya ci tura, saboda rashin samun goyon bayan mahaifiyarku. Karshe ma Hauwa ta dauketa ta boyeta ba tare da na san inda ta kai ta ba, don haka na, Kiraku domin na gaya maku Afrah ta share min, hawayena ta amince za ta auri Dan-uwanta, shi ya sa na kiraku domin na shaida maku, na ba Musaddik Afrah, na kuma sanya ranar bikinsu uku ga sabon wata me kamawa”,
Mama Hauwa ta yi karaf! Ta amshe cike da farin-ciki “ Alhamdulillah, wai hankalina har ya kwanta. Allah ya ba su zaman lafiya, yanzu ka yi magana, dama Na'ima ai ba ta yi dai-dai da shi ba ita ma Afrah ta gama kinibibinta matsalarku, ni dai tunda Allah ya kubutar da 'yata komai ya yi dai-dai “ Mansur ya kalli Kabir sannan ya dubi Malam Mahmud ya ce”Amma baba anya kana ganin wannan lamarin me yuwuwa ne kuwa?” Ya gyada kai yace “kwarai kuwa mansur me ka gani Mansur. ya gyara zamansa yace “Baba gani nayi kamar ba’ayi mata adalci ba ba hadata aure da