Musabbabi Book 1

Page 50

by @yargidanimam

da mutum irin Musaddik. Baba ko yanzu da zan taho nan na hadu da shi yana rangaji alamar a buge yake, gaskiya ina ganin bai kamata a hada su aure ba, domin babu ta inda suka dace, halayen Musaddik a gaskiya sun kazanta ." Kabir ya amshe naganar “Kwarai kuwa Baba, idan aka aura ma Afrah Musaddik, gaskiya ba'ayi mata adalci ba, ba za ta iya zaman rayuwa da shi ba. Baba kai ma ka san ko waye Musaddik, gaba daya aure ma bai dace da shi ba, domin babu Macen da zai iya rikewa, don Allah ka janye wannan maganar baba”. Malam Mahmud ya numfasa ya ce “Na ji dadin yadda ku ka damu da rayuwar kanwarku, sai dai ku sani, ina da manufar hada auran Afrah da musaddik Tunda kuma ta yarda ta ba ni goyon baya, babu abinda zai canja, uku ga wata zan daura auransu, idan lallai kun damu da ita, to ku tayata addu'ar Allah ya ba ta ikon cinye jarabawar daya dorata akai" mansur yace “Amma ….bai karasa ba Mama Hauwa ta katse shi "Kai ya isheku, ba "Yarsa bace, yana da damar da zai yi duk abinda ya ga damar yi da ita, ina ruwanku" Mallam Mahmud ya yi mata wani irin kallo me cike da tsana ya ce "Ni ban sa maganar nan da ke ba, ban gayyatoki cikinta ba, don haka zai fi sauki ki rufe bakinki tunda ba maganar yarki Na’ima ake yi ba, kamar yadda kika fada ne ya ta ce yar kuma da nake alfahari da ita”.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam

Kuyi comments domin karfafa guiwa MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM