Page 51
Mama Hauwa ta saki tsaki ta cc "Dama ai ban ce ya shafe ni ba, ka ga wanda ya shafenin ai na hana, na kuma dauke "yata, goben nan kuma za ta dawo gidan ubanta. Allah ya kawo mata miji nagari, ba tambadadde irin Musaddik ba.” Ta mike ta shige dakinta, a yayin da Mallam Mahmud ya dubi su Mansur cikin Bacin ran maganganun Mama Hauwa ya ce “Ita kenan maganar, ku na iya tafiya, Allah ya ba mu alheri” Yana gama fadin haka ya tashi ya shige dakinsn, ya bar su nan zaune suna kallon juna, daga bisani su ma suka tashi suka shiga dakin mahaifiyarsu . Suna shiga Mama Hauwa ta hau fada “Ina ruwanku da za ku hana shi hada auran Afrah da mahaukacin dansa, can su suka sani, meye naku Shi ya fi kowa sanin waye Musaddik, Kuma ita kanta wacce ku ke kokarin kwato mata "yancin, na Yancin na yi imanin kunya za ta ba ku, don Yadda na san wannan kinibabbiyar yarinyar. To ba za ta taba kauce ma umarnin Mallam ba, matukar dai ya bude baki ya nemi ta auri Musaddik, to tabbas duk duniya babu wanda zai hana hakan faruwa, sai dai Allah, don haka ban ga amfanin sanya bakinku cikin wannan maganar ba