Musabbabi Book 1

Page 52

by @yargidanimam

Mansur ya kalleta ya ce “ mama rayuwar Musaddik kullum kara lalacewa take yi, babu wani abun burgewa ko kadan a rayuwarsa. Ko wacce ba ni wacce ba ni da dangantaka da ita, ba zan so ta aure shi ba domin na san rayuwarta ta gama lakacewa Balle jinina kanwata Mama, amma tunda ba’a bukatar gudunmuwar shawararmu, to Allah sanya alheri, fitinar da ke ciki. Allah ya Kare Afrah kuma Allah ya kawo mata mafita." Ta yi masa wani sakaran kallo ta ce “To Shehin Malami, addu'ar taka ta yi, Allah ya karba akaramakallahu” Kabir ya ce "Ai Kabir ya dubeta yace “Ai duk maganganunsa gaskiya ne. Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri" Gaba dayansu suka tashi ba su damu da hararar da take banka masu ba, suka yi mata sai da sale, suka kama hanyar gida. Ita ko Mama Hauwa zuciyarta cika ta yi da tsananin farin-ciki, dama ba ta taba yi ma Afrah fatan samun miji na-gari ba, burinta ya cika Afrah za ta yi auran wahala, •ta yi wani bushasshen murmushi, domin dukkan mafarkinta akan Afrah ya kusa tabbata. Ta lalubo wayanta da ke kasan filo, ta kira lambar Na'ima, tana dauka, bayan sun gaisa ta tace “ Na'ima ki shirya gobe ki dawo gida. Cike da son karin bayani Na’ima tace "Na dawo gida Mama? Babu sauran matsala kenan”.