Musabbabi Book 1

Page 53

by @yargidanimam

Mama Hauwa cike da fara’a tace "Eh, ki dawo gida, saboda komai ya wuce maganar auranki da Musaddik an maida shi Kan Afrah Na'ima ta ce "Mama kan Afrah, ta Kuma yarda ta amince?" Mama Hauwa ta yi dariya sosai tace “Tana da za6i ne? Ai in dai akan mhaifinta ne, ba ta da zabi, duk abinda yake so shi take so, ko da ba ta so, ko kin manta halinta ne kinibabbiya ce mai kokarin maida kanta mara "'yanci, saboda farin-cikin mahaifinta, don haka ta yarda, duk kuma abinda zai biyo baya, wannan ruwansu, su ta shafa" Na'ima ta ce "Amma lallai Afrah ta shiga tara ma ba uku ba". Mama Hauwa ta ce "Idan ana Shiga dari ma, to ta shiga, auran mashayi sakarai wanda bai san darajarsa ba balle ya san darajar wani" Na'ima ta ce "Lallai kam!" "Saboda haka ki tattaro ki dawo, dama kadaicin rashinki duk ya ishe ni”, cike da murna Na’ima tace “zan dawo goben nan kamar yadda ki ka ce mama “, daganan su kayi sallama, kowa cike da farincikin kawo karshen matsalar su.