Page 54
Gida ne katon gaske mai kyakkyawan fasali, Kallo daya za ka yi masa, ka tabbatar da cewa gida ne na masu hannu da shuni, gidan marigayi Alh Mansur maifata kenan. Hajiya Kilishi na zaune akan daya daga cikin kujerun da suka mamaye katon falon nata, idonta dore akan akwatin Talabijin. Sallamar Musaddik ya sa ta kalli kofar falon ba tare da ta amsa sallamar ba.
Shi ma bai jira ta amsa ba, ya shigo lokaci daya, ya zauna yana kokarin gaisheta, ta amsa kamar kullum ranta a bace, fuska ba walwala, "Daga ina ka ke yau kwana biyu kenan rabon ka da gidan nan “ ya kaskantar da kansa yace “Haj ayi hakuri aiki ne kawai ya yi min yawa” tayi masa wani irin kallon banza tace “Aiki ?har wane auki ka ke da shi, kana dai can yawon gantalinka da ka saba, ai ba hanaka zanyi ba Allah ya bada sa’a”. Musaddik ya numfasa, duk da baya jin dadin yadda Hajiya Kilishi take bi da shi, to fa bai hana shi yi mata biyayya tare da tsoron bacin ranta ba bai kuma taba kallonta a matsayin mai kinsa ba asalima tana daya daga cikin Mutanen da Yake tsananin ganin girmansu tare da. ganin mutuncinsu . Ya dago yana kallonta, a yayin da ta maida kallonta kan akwatin Talabijin dinta, tana fadin