Musabbabi Book 1

Page 55

by @yargidanimam

"*Idan yunwa ce ta kawoka, ka shiga kicin ka debi abinci, don Lami ta fita balle ta kawo maka Ya girgiza kai ya ce “A’a Haj a koshe nake magana dai na zo muyi da ke” ba tare da ta kalle shi ba tace “wace irin magana ce?” Ya dan muskuta ya gyara zamansa, sannan ya ce "Magana ce mai muhimmanci akan aurena da da ya gabato”, A gaggauce Hajiya Kilishi ta juyo ta kalle shi, hankalinta a tashe, kamar wacce aka gaya ma sakon ranar mutuwar ta "Auranka?" Ta maimaita a tambayance, ya daga kansa ya ce "Eh, Kawu Mahmud shi ne ya ba ni auran Yarsa Afrah, ya kuma sanya ranar daurin auren uku ga watan da zai kama, shine ya ba ni damar na zo na sanar da ke.....?" Ta katse shi a matukar fusace ta ce "'Ka zo ka gaya min a matsayina na wa, me na isa, sannan meye amfanin gaya min, tunda har sai da ku ka gama kulla komai sannan aka turoka ka gaya min To meye amfanin gaya min? Musaddik ya rude, a dalilin ganin 6acin ranta ya ce "Don Allah ki yi hakuri Hajiya. Kada ki sa damuwa akan wannan maganar, ni kaina a Kurarren lokaci aka gaya min, sannan babu wani bata lokaci ya sanya ranar “ Ta sakar masa harara cikin hadewar fuska da wani bakinciki ta ce” a kurarren lokaci ai komai kurewar lokaci, don me ba za ka iya zuwa ka gaya min ba?