Page 56
tabbas akwai wani abun da Mallam Mahmud ya hanga yasa yake son hada auranka da Afrah , domin tabbas! Aure a yanzu bai dace da kai ba, illa iyaka wata manufa da yake da ita, to bari kaji idan yana tunanin dan abinda ya rage maka na daga gadonka ne yake son ya hada auranka da 'Yarsa, don su kwashi rabonsu. Ai ya kamata ka yi masa bayanin cewa ba ka da sauran komai, domin abinda ya ragen ka dade da cinyewa, wasu ka sayar , ka yi shayc-shaye da kudin, babu abinda yarsa zata aura sai musaddik tsurarsa da wahalarsa “. Hankalin musaddik ya tashi ko kadan baya jin dadin maganar da Hajiya Kilishi take yi ta cin fuska da wulakanci, ga kawunsa. ya yi Kasa da kansa, ransa na kuna, a yayin da ta cigaba da magana “Ni wannan yarinyar ko kadan ba ta burge ni, ba ta taba ba ni sha'awa ba , don haka bana murna ko maraba da auranka da ita". Ya dago ya kalleta sosai sannan yace "Hajiya ke ce mutum na farko a duk duniya da na taba jin kin ce Afrah ba ta burge ki, domin Afrah tana burge kowa, ko ba don kyawun fuskarta ba, don kyawun halayenta da natsuwarta, dole ta burge kowa”, Hajiya Kilishi ta ce tana yi masa wani mugun kallo “ Wato ka na son auranta kaima ko Musaddik, ba shirin Kawunka bane kadai, kai ma ka na so” Musaddik ya hadiye bacin ransa ya ce