Page 57
“Aure baya gabana ba na kuma yi ma kaina sha’awar zama shugaban kowace mace. Domin na san ba zan iya yi mata adalci ba, amma zuciyata na sameta cike da dokin auran Afrah, don haka ke ma ki amince da ita, domin alfarma za ta yi min na aurena.” Yana gama fadin haka ya tashi ba tare da ya saurari komai ba daga gareta , ya fice ransa da hankalinsa a tashe Bakin-ciki da tsananin damuwa suka Kara cika zuciyar Hajiya Kilishi. Ta tashi ta shiga kai gauro ta kai mari a tsakiyar falon, ko kadan ba ta bukatar Musaddik ya Kara yin aure, domin tana da tabbacin idan ya yi aure ranta na bata Dole ya rage wani abu daga cikin ta'asar da yake yi, wanda ba za ta taba son hakan ba, kuma auran nasa zai zama sanadiyyar da zai samu shi ma ya kafa tasa zuri'ar, sannan ko yaya ne za 'a dinga ganin mutuncinsa, abinda bata so kenan amma tunda yana da iyali, ko ya ya ne sai an samu me dan ganin mutuncinsa . hakika auran Musaddik fitina ne a gareta, don ranta baya so. Kuma abu ya zo gaba daya cikin kurarren lokaci, amma gaskiya dole ta yi wani hobbasa akan kokarin watsa auran tun kafin ayi, gara Musaddik ya zauna ya ci-gaba da gurbatacciyar rayuwarsa ta yi imanin kuma babu macen da za ta tattagoma kanta auran shashasha irinsa, In dai ba irin wannan auran zumuncin ba na sadaukarwa Babu ta inda za'ayi Musaddik samu auran wata mace a irin lalacewar rayuwar da ya ke ciki.