Musabbabi Book 1

Page 58

by @yargidanimam

shin ya aka yi Malam Mahmud ya yi tunanin yi ma musaddik aure da yarsa kuma meye manufarsa?”. Domin dai ta fi kowa sanin cewa Mallam Mahmud ya san Musaddik bai aje ba, bai ba Wani ajiya ba balle ta yi tunanin don abin duniya Yake son ya hada auran nasu, kamar yadda ta fadawa musaddik hakika wannan abu bai yi mata dadi ba kwata-kwata.

Hakan ya sa gari na yin sanyi, karfe biyar da rabi dai-dai motarta ta tsaya a kifar gidan Mallam Mahmud, ga sa'arta kuma Malam Mahmud din yana gida bai dade da dawowa-gidan ba,mama Hauwa ce ta tareta “Hajiya Kilishi ce da yamman nan? “ Cewar Mama Hauwa, tana kokarin aje tsintsiyar hannunta, da take kokarin tattara gudan da ita Hajiya Kilishi ta ce fuska tamke “Nice Hauwa” Mama Hauwa tace “ shigo mana daga cikin daki Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zama na zo yi ba, sauri na ke na koma gida, wajen Mai gidan na zo, ina fatan yana nan" Mama Hauwa ta yi murmushi dimin ta fahimci Hajiya Kilishi bada arziki ta zo ba, ta san kuma dama ba wata jituwa ce tsakaninta da Malam Mahmud ba, don haka tace “yana nan” Kafin ta yi magana. Malam Mahmud ya fito daga dakinsa yana kallon Hajiya Kilishi yace "Sannu da zuwa" da sauri ta juyo ta kalle shi ta amsa "Yawwa, ina gajiya?" "Lafiya Kalau, hala dan naki ya gaya miki sakona ne?"