Page 59
Tace cukin kara hade rai “eh ya zo ya sanar da ni dazu shine dalilin zuwana ma yanzu”Yace “Toh” .Hajiya Kilishi ta gyara tsayuwarta, sannan ta fara nagana “Yanzu tsakani da Allah wannan abin an yi dai-dai kenan?" Ya ce *Kamar yaya?" Ta ce “Kamar na yadda za'a gaya mana magana daga sama, ni dai a'iya sanina Musaddik da Afrah ba sa soyayya, haka zalika bai taba yin min maganar yana son ya Kara yin aure ba, tun bayan rabuwarsa da Hannatu, don haka na yi mamakin jin lamarin. Kuma wane abu ne ya sa ka tunanin kulla wannan auran? Bayan kana sane da halin da yake ciki, auran ma ba zai iya rikewa ba. Don haka ina ganin maganar auran nan a bar ta kawai har zuwa lokacin da zai sami natsuwa, ya nemo 'yar da yake so da kansa” Malam Mahmud ya jinjina kai cikin wani irin Yanayi yace “wace irin magana ce wannan ki ke yi, shin meye amfanin sanya ma Musaddik ido ya Ki yin aure, don kawai ana kallonsa a matsayin dan iska Wanda ke kin sani , ni na sani jama'ar ma da suke yi masa kallon hakan sun san cewa da ba haka yake ba, kaddarar rayuwa ta maida shi haka. To don me ba za mu taimake shi ba, ni zumunci na ke ma, domin Musaddik ba shi da bambanci da dan da na haifa, tunda "Yar-uwata ce ta haife shi, don haka ko ta wane hali, dole na taimaka ma rayuwarsa, zan kuma aura masa Afrah