Page 60
ne , domin ya samu mai kulawa da shi da kuma rayuwarsa. Don haka maganar a janye wannan auran ba za ta yiwu ba, domin mun riga mun gana yanke magana.” Hajiya Kilishi ta yi tsaki ta ce "Ka na wani daga murya sai ka ce wanda aka zo yin fada da shi ni ba fada ya kawoni ba, rayuwar "yarka da na ga kana so ka lalata, shine na ke son na fahimtar da kai kuskuran hakan, idan kuma da manufarka ta daban ne to ka yi ganganci. Domin ka fi kowa sanin Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, ina tsammanin wurin zama ma, sai dai idan na ga dama na ara masa, daki haka idan ka na tunanin abin duniya ne, ya sa ka ke Kokarin cuso "'yarka, to ka yi kuskure..... Ya dakatar da ita rai a matukar bace ya ce “Kada ki Kara yi min wannan maganar, wane arziki zaki gaya min, ke ce ke hadamar arzikin Musaddik tunda kuma kun gama cinyewa ke da Yar’uwar ki Hannatu, ba shi kenan ba, ku je ya yi Maku arzikn duniya da lahira, yadda kuma Hannatu ta bar shi shine ku ke tunanin ba wacce za ta iya auransa, to kunyi kuskure Auran Afrah da Musaddik ko bayan raina ne, sai anyi shi, kuma za ta zauna da shi ko da shi ya fi kowa talauci da lalacewa, domin na isa da 'Ya ta, za kuma ta share min hawayena tun kafin ya zuba”.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM ✍️