Musabbabi Book 1

Page 61

by @yargidanimam

Haj kilishi ta kara fusata tace "Eh, Hannatu ta bar shi, don bai dace da ita ba, dukiya kuma da ka ke magana da kansa ya bayar, don haka ba dalilin maimaita maka, 'yarka ko ka yi ta aura masa, ina kuma taya yarka murnar auran musaddik, ina mata barka da fadowa rayuwa mai cike da nadama da danasani ". Daga nan bata jira komai ba ta juya a fusace za ta tafi. Dai-dai zaure suka ci karo da Afrah, ta tsaya ta yi mata wani mummunan kallo, Sannan ta fice ba tare da tace mata uffan ba Jikin Afrah a sanyaye ta shigo cikin gidan, ganin fuskar mahaifinta a dagule ya tabbatar mata da cewa ba abin arziki ya kawo Hajiya Kilishi gidansu ba, ta kalli Mama Hauwa ta ga sai Fara’a take, tana harkarta. Afrah ta dawo da Kallonta ga mahaifinta ta ce a sanyaye "Baba make faruwa ne, naga Hajiya Kilishi a fusace ta fita?"mallam mahmud ya yi gaggawar boye damuwarsa, yace “A’a Afrah lafiya kalau, na kirata mun yi magana ne a kan auranki da yayanki”, Mama Hauwa ta yi karaf! Ta ce "Me ya sa ba za ka gaya mata gaskiyar cewa Hajiya Kilishi ba ta son auranta da Musaddik ba, kuma ta yi maka maganganu na wulakanci da batanci wanda ta saba” A kidime Afrah ta dubi mahaifinta ta ce "Wulakanci da Batanci akan me? Wace ce ita da har take da dama da garantin tsayawa a gaban mahaifina ta yi masa wulakanci?” Mallam Mahmud